#wasu kuma na cewa yin sak yana daya daga cikin abubuwanda zasu iya fadawa rami.
TOH MENENE YA DACE?????
JAM'IYYAH: wata inuwa ce da yan takara suke shiga su labe domin a zabe su su hau mukaman da suke so.
Bata da wani tasiri ga wanda ya tsaya acikinta. Hakan ne ma yasa wasu yan takarar suke canja jam'iyya yayinda suka hau mulkin.
NAGARTA: wani kyakkyawar siffa ce ta shugaban da yadace azaba koda a wacce zam'iyya yafito kokuma ya fito takara ne a kashin kansa (Independent) ba a karkashin kowace jam'iyya ba.
BUHARI YACE MUYI SAK.....
Muna godewa Allah madaukaki daya zabar mana Janar Muhammadu Buhari, domin shine muke sarai zaiyi mana adalci a wannan kasar tamu. Allah ya tayashi riko.
Amma Nasan cewa Shi Janar Buhari ya fadi wannan magana ne a matsayinsa na dan jam'iyyar APC, kuma dokane ya tallata wata jam'iyya ba tashi ba.
Amma nasan in zaka tambayeshi cewa dukkan yan takarar APC mutan kirki ne?? Wallahi zaice maka A'A. Toh babanmu (buhari) tayaya zamu zabi na kirki da wadanda ba na kirki ba???
ANNABI SAW fa yace: idan aka baka zamin mutane 2, kasan ga wanda yafi cancanta amma kazabi wanda bashine ya cancanta ba sai Allah yayi maka hisabi akan hakan.
KU ZABI MUTANEN DA SUKA CANCANTA
Koda kuwa a wacce jam'iyya suke.
A APC: akwai yan takara na kirki, ku zabe su.
A PDP akwai yan takara na kirki ku zabe su.
A APC akwai bara-gurbin yan takara, kada ku zabe su.
A PDP Akwai bara-gurbin yan takara, kada kuzabe su.
ALLAH BAZAI TAMBAYEKA JAM'IYYAR DAKA ZABA BA.
Domin ba itace mai muhimmanci ba, amma Allah zai tambayeka WA ka zaba.
TANBIHI:
Kuyi adalci katange wannan rubutun da rubutun siyasa, domin wannan ba aikinmu bane, kuma in ka fahimta a nutse zakaga ba wani akewa talla ba, gaskiya kawai ake tallatawa kamar yadda aka saba.
Zaku kara jina.
Awaisu Al'arabee Fagge
9-4-2015 SALLAMA A MUSULUNCI
Bayan haka; ina yiwa yan uwana musulmi sallama irinta addinin islama, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Nayi nufin yin wannan rubutun ne domin sakaci danaga al'uma sunayi gameda sha'anin sallama, kuma gata aba ce mai matukar muhimmanci, bai kamata a watsar da ita ba.
Ina fata rubutu na zai wayar da kan mutane gameda hakan.
Allah yasa mudace.
SASHI NA DAYA
MATSAYI DA FALALAR SALLAMA
بسم الله الرحمن الريم وصلي الله على النبي الكريم
Yana daga cikin kyawawan dabi'u wadanda addininmu ya karantar damu 'yadawa da yawaita sallama a junanmu' (mu musulmi).
Allah yace: وَإِذَا جَاءَكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِنَا فَقُلْ سَلَامٌ عَلَيْكُمْ
Ma'ana: idan wadanda sukayi imani da ayoyinmu sukazo maka to kace musu aminci yatabbata agaresu (sallama)
Kaga kenan saboda matsayin sallama a musulunci har Allah madaukaki yayiwa manzonsa umarni da yinta.
Saboda matsayinta itace sallamar yan aljanna idan sun shiga
Allah yace: دَعْوَاهُمْ فِيهَا سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمْ فِيهَا سَلَامٌ وَآخِرُ دَعْوَاهُمْ أَنِ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Ma'ana:- Allah yace (gameda yan aljanna) "idan sunaso ko kuma suna sha'awar wani abu toh kiranda zasuyi shine subhanakallahumma' sannan kuma gaisuwarsu shine salam, sannan maganarsu ta karshe bayan sun gama ci ko shan abinda suka bukata shine suna cewa alhamdulillahi rabbil alamin" (kamar yadda abdullahi bn abbas yafassara)
Sannan sallama wata kalmace da ake amfani da ita yayinda akeso a rarrashi mutun ko a bashi girma. Misali
Allah yana bamu labarin abinda yafaru tsakanin annani Ibrahim dashi da mahaifinsa lokacinda yaje yi masa wa'azi.
Allah yace:- قَالَ سَلَامٌ عَلَيْكَ سَأَسْتَغْفِرُ لَكَ رَبِّي
Ma'ana: (baban annabi ibrahim yayi masa wa'azi sai mahaifin yadauki zafi shikuma sai yakeso ya yarrashe shi) sai yace masa aminci yatabbata agareka (sallama) kuma dasannu zam roka maka gafarar ubangiji na.
-----------zamu cigaba inshaAllah
Yana daga cikin darajoji da muhimmancin sallama da Allah yasanyata itace gaisuwarda annabawansa da mala'ikunsa suke amfani da ita a junansu. Misali;
Allah yace; وَلَقَدْ جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَى قَالُوا سَلَامًا قَالَ سَلَامٌ
Ma'ana: haqiqa manzanninmu/yan aikenmu (mala'iku) sunjewa annabi ibrahim da bushara, toh dasuka zo sai suka ce masa 'salam' (salamun alaikum) shima sai ya amsa musu sa 'salam'.
Muhimmancin sallam ne yasa Allah madaukaki ya singa amfani da ita domin sanyawa annabawansa albarka a cikin suratu saffat
Allah yace سَلَامٌ عَلَى نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَ.
Ma'ana: aminci yatabbata annabi Nuh
Allah yace: سَلَامٌ عَلَى إِبْرَاهِيمَ
Ma'ana; aminci ya tabbata ga annabi Ibrahim
Allah yace: سَلَامٌ عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ
Ma'ana: aminci ya tabbata ga annbi Musa da annabi Haruna
Allah yace: سَلَامٌ عَلَى إِلْ يَاسِينَ
Ma'ana : aminci ya tabbata ga annabi ilyas
Duk wadannan ayoyi idan kalura zakaga cewa ubangiji ne yake yiwa annabawansa salllama.
Sannan ita dai sallama itace kalmar da mala'iku masu tsaron kofar aljanna zasuyi wa muminai yayinda sukaje shiga aljanna akaro nafarko.
Allah yace: وَسِيقَ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ إِلَى الْجَنَّةِ زُمَرًا حَتَّى إِذَا جَاءُوهَا وَفُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا سَلَامٌ عَلَيْكُمْ طِبْتُمْ فَادْخُلُوهَا خَالِدِينَ
Ma'ana : za'a raka wadanda sukaji tsoron ubangijinsu a dunia izuwa aljanna a kungiyance, yayinda sukaje kofar aljanna sai abude kofofinta, sai masu tsaron aljannna suce musu aminci ya tabbata a gareku (sallama), yabo ya tabbata gareku, ku shiga aljanna kuna masu dawwama acikinta.
Wannnan kadanne daga cikin falaloli da suka zo gamedda sallama a cikin alqur'ani mai tsarki/girma
Bisa qa'idar ahlussunnah aljama'ah, suna yin abubuwansu ne bisa la'akari da ayiyon qur'ani da hadisan manzo rahama S.A.W saboda haka yanzu kuma zamu juya bangaren hadisan annabi domin mu duba sukuma mai suka kawo mana gameda falala, muhimmanci da darajar sallama a musulunci.
A lokacinda Allah ya halicci babanmu Annabi Adam umarnin da Allah yafara bashi shine na yin sallama. Ga hadisin kamar haka:-
قال أبو هريرة: كان أول ما جرى فيه الروح من آدم، بصره وخياشيمه، فلما جرى الروح منه في جسده كله عطس، فلقاه الله حمده فحمد ربه، فقال الله له: رحمك ربك، ثم قال الله له: اذهب يا آدم إلى أولئك الملأ فقل لهم: سلام عليكم، فانظر ماذا يردون عليك، ففعل ثم رجع إلى الجبار، فقال الله له، وهو أعلم: ماذا قالوا لك؟ فقال: قالوا وعليك السلام ورحمة الله، فقال له: هذا يا آدم تحيتك وتحية ذريتك.
ma'ana: an karbo hadisi daga Abu hurayra yace "( yayinda Allah yabusawa Annabi Adamu rai) ran yafara shiga ne ta idonsa da karan hancinsa, toh bayan ran yagama kewaye gaba daya gangar jikinsa sai annabi adamu yayi atishawa, sai Allah ya laqanta masa hamdala (alhamdulillah) sai annabi adamu yafada. Sai Allah yace masa ubangijinka yayi maka rahama (rahimakallah). Sannan sai Allah yace masa yakai Adamu kaje wajen wadancan al'ummar (mala'iku) kace musu salamun alaikum (salama) sai kajira kaji mai zasu amsamaka dashi, sai annabi Adamu yaje ya aikata abinda Allah yamasa umarni dashi. Daya dawo sai Allah yatambaye shi (alhalin shine mafi sani) yakai Adamu mai suka ce maka? Sai annabi Adamu yace danayi musu sallama sai sukace min wa'alaikumussalam warahmatullah, sai Allah yace to wannan itace gaisuwarka dakai da zurriyarka."
(dabaqatul kubra na ibn sa'ad. Uz'i na 1 shfi na 301)
Muhimancin sallama bai takaita kadai akan masu rai ba. a'a har musulmi wadanda suka riga mu gidan gaskiya suma anayi musu sallama yayinda akaje inda suke kwance (maqabarta) kamar yadda ya tabbata a hadisi ingantacce kamar yadda zaizo
عن أبي هريرة قال : خرج رسول الله صلى الله عليه و سلم إلى المقبرة فسلم على أهلها وقال : سلام عليكم أهل دار قوم مؤمنين وإنا إن شاء الله بكم لاحقون
Ma'ana: an karbo hadisi daga abu hurayra, yace "watya rana annabi yafito zai tafi izuwa maqabarta, toh dayaje sai ce '' aminci yatabbata gareku(sallama) ya ma'abota gidan muminai (ma'abota maqabarta) kum dasannu muma zamu gamudaku "
(sahih ibn kuzaima, juz'I na 1 shafi na 7)
To tinda akayiwa matacce sallama to ai wand yake da rai shine yafi cancanta da ayi masa sallama.
Sallama itace kalmarda yakamata mutum ya dinga amfani da ita domin gaishe da mutane na gida ko na waje. Idan kai maigida ne to sai kayi koyi da mai gidanda yafi kowane mai gida iya zama da matan gida.
Yatabbata a hidisi ingantacce cewa annabi yana gaishe da iyalinsa ne da sallama kamar yadda zaizo
قَالَ أَنَسٌ وَشَهِدْتُ وَلِيمَةَ زَيْنَبَ فَأَشْبَعَ النَّاسَ خُبْزًا وَلَحْمًا وَكَانَ يَبْعَثُنِى فَأَدْعُو النَّاسَ فَلَمَّا فَرَغَ قَامَ وَتَبِعْتُهُ فَتَخَلَّفَ رَجُلاَنِ اسْتَأْنَسَ بِهِمَا الْحَدِيثُ لَمْ يَخْرُجَا فَجَعَلَ يَمُرُّ عَلَى نِسَائِهِ فَيُسَلِّمُ عَلَى كُلِّ وَاحِدَةٍ مِنْهُنَّ « سَلاَمٌ عَلَيْكُمْ كَيْفَ أَنْتُمْ يَا أَهْلَ الْبَيْتِ ». فَيَقُولُونَ بِخَيْرٍ يَا رَسُولَ اللَّهِ كَيْفَ وَجَدْتَ أَهْلَكَ فَيَقُولُ « بِخَيْرٍ ».
ma'ana: ankarbo hadisi daga Anas dan malik R.A yace " naje walimar Zainab, mutane sukaci gurasa da nama, annnabi yakasance yana aikani domin in kira mutane domin su halarci walimar. Yayinda annabi yagama walimar sai ya miqe nikuma ina biye dashi, sai wasu mutane guda biyu sukayi zamansu suna ihira, su basu biyo mu ba. sai manzon Allah ya dinga zuwa dakunan matayensa yanace musu ' amincin Allah ya tabbata gareku (sallama) yaku ahlulbaiti yakuke???' sukuma sai kuke amsa masa da cewa da alkhairi,…………."
(sahih muslim 3572)
To wannan kadan kenan na abinda hadisai suazo dashi gameda sallama.
Idan bazaku mantaba tun daga farkon rubutuna inata kawo falala da matsyine na ita sallama. Yanzu kuma zan juya sashi na biyu na wannan rubutun.
SASHI NA BIYU
MA'ANAR SALLAMA:
Ita dai kalmar 'salam' kalma ce ta larabci. Fasssararta ahausa shine aminci. Sanin kowa ne cewa aminci shine zaman lafiya tsakanin al'umma.
Sannan kuma ita kalmar salam daya ce daga cikin sunayen Allah madaukaki. Kamar yadda zamu kawo jerin ayoyin da tazo a cikinsu. ,misali
هُوَ اللَّهُ الَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْمَلِكُ الْقُدُّوسُ السَّلَامُ الْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ الْعَزِيزُ الْجَبَّارُ الْمُتَكَبِّرُ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Wannan ayar dai naan bata bukatar wani karin bayani ko fasara.
Amma idan muka kula zamuga kalmar tazo ne a sunan Allah
Sannan kalmar tana zuwa da ma'anar sunan aljanna. Misali
Allah yace
لَهُمْ دَارُ السَّلَامِ عِنْدَ رَبِّهِمْ وَهُوَ وَلِيُّهُمْ بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Ma'ana: su(muminai) suna da gida na aminci a wajen ubangijinsu, sannan shine majibincin lamarinsu bisa abubuwanda suke aikatawa.
Kunga anan kuma kalmar tazo da ma'anar aljanna.
Wannan fa duk ana magana ne gameda kalmar salam ita kadai. Idan kuma kadauki ma'anar sallamar gaba dayanta zaka samu abubuwa karkashinta. Zamu kawo kadan daga cikin.
Yazo acikin asar na sufyan bin uyainah kamar yadda zaizo
أَنْبَأْنَا مُحَمَّدُ بْنُ عَلِيٍّ ، سَمِعْت أَبِي يَقُولُ : قَالَ ابْنُ عُيَيْنَةَ : أَتَدْرِي مَا السَّلَامُ ؟ تَقُولُ : أَنْتَ
مِنِّي آمِنٌ
Ma'ana; sufyan bin uyainah yake tambayar wani yace masa, idan nace maka salamun alaikum kasan mai nake nufi?
Sai yace a'a, sai yace masa idan nace maka salamun alaikum ina nufin ka aminta a gareni.
(ahkamul qur'an na ibnul arabee. Juz'I na 2 shafi na 382)
SASHI NA UKU
A yanzu kuma zamu shiga magana ne gameda wanda yakamata ayiwa sallama da wanda bai kamta ayiwa sallama ba.
Duk da irin matsayin sallama da muka ambata abaya fa bai ba kowan ake yiwa sallama ba sai de wanda shari'ah tabada dama ayi masa.
Shi dai musulmi anayi masa sallama kai tsaye, karamin e ko babba, namiji ne ko mace, aqidarku daya kokuma akwai banbanci, ahlussunnah ne ko dan bidiah, kowanne anan shari'ah tabada dama ayi masa sallama. Wani zaice menene hujja gameda hakan. Sai ince saboda Allah ne yafadi hakan a littafinsa mai tsarki.
Allah yace: وَإِذَا جَاءَكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِنَا فَقُلْ سَلَامٌ عَلَيْكُمْ
Ma'ana: idan wadanda sukayi imani da ayoyinmu sukazo maka to kace aminci ya tabbata garesu (salllama)
Amma shi kafiri bai halatta ayi masa sallama ba, shari'ah tahana. Idan nace kafiri ina nufin mushrikai, wadanda basu bautawa komai, masu aikata babban munafurci, yan shia da sauansu.
Wani zaice maiyasa nakawo yan shi'ah a sahun kafirai?
To ai basa yadda da wasu daga cikin ayoyin Allah, kaga kuwa duk wanda bai yarda da ayar Allah ba toh ya kafirt koda kuwa ayar daya ce. Sannan manyan malamai sun tabbatarda kafircin dan shi'ah.
Idan kayi duba wasiku ko takardu da shigabannin musulmai suke aikawa sarakuna da masu mulkin kafirai zakaga ba'ayi musu sallama sade ayi musu jirwaye da kamar wanka. Misali: lokacinda manzon \allah ya aikawa shugaban kasar rum wasika aciki sai yayi amfani da wani salo daya kamata yi amfani dashi yayin yiwa kafiri sallah. Ga yadda wasikar take:
بسم الله الرحمن الرحيم من محمد رسول الله إلى هرقل عظيم الروم سلام على من اتبع الهدى
Ma'ana: da sunan Allah mai rahama mai jin kai, wannan wasika ce daga Muhammadu manzon Allah zuwa ga hiraql maimulkin rum. Aminci ya tabbata ga wanda yabi shiriya (musulunci).
Kaga annabi baice aminci ya tabba a gareshi ba, sai yace ga wanda yanemi/yabi shiriya.
Sannan lokacinda annabi ya aikawa da kisrah wasika anan ma yayi amfani da wannannsalon kamar yadda zaka gani a rubutun.
من محمد بن رسول الله إلى كسرى عظيم الفرس ... سلام على من اتبع الهدى وآمن بالله ورسوله
Ma'ana: (wannan wasika ce) daga Muhammadu manzon Allah zuwa ga kisrah mai mulkin kasar Faris. Aminci yatabbata ga wanda yabi shiriya sannan yayi imani da Allah da manzonsa.
Sannan haka zaka gani a wasikar da annabi ya mayarwa da musailamatul kazzab a lokacinda ya aiko masa da wasika. Ga takardar kamar haka:-
من محمد رسول لله إلى مسيلمة الكذاب سلام على من اتبع الهدى، أما بعد فإن الأرض لله يورثها من يشاء من عباده والعاقبة للمتقين
Ma'ana: (wannan wasika ce) daga Muhammadu manzon Allah zuwa ga musailama taceccen makaryaci. Aminci ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka; hakika ita kasa ta Allah ce kuma yana gadar da ita ne ga wand yaga dama daga cikin bayinsa. Sannan kyakkyawan karshe na masu tsoron Allah ne.
Haka kuma idan ka koma alqur'ani mai girma zakaga irin wannan sallamar annabi Musa yayiwa fir'auna a lokacinda Allah ya aikashi wajensa.
Allah yace
فَأْتِيَاهُ فَقُولَا إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ وَلَا تُعَذِّبْهُمْ قَدْ جِئْنَاكَ بِآيَةٍ مِنْ رَبِّكَ وَالسَّلَامُ عَلَى مَنِ اتَّبَعَ الْهُدَى
Ma'ana: Allah yacewa annabi Musa da Haruna kuje kucewa fir'auna mu manzonnin ubangijinka ne. kuma kasani bani isra'ila mutafi taredasu izuwa kasarda Allah yamana umarni. Kuma kadena azabtar dasu. Hakika munzo maka da shiriya daga wajen ubangijinka. Aminci yatabbata ga wanda yabi shiriya.
(kamar yadda ibn Abbas ya fassara)
SASHI NA HUDU
YADDA AKE FURTA SALLAMA
Dayake ni bahaushe ne, zan iya cewa yawancin kabilata basu iya sallama ba. yawanci zakaji suna cewa 'salama alekum' Allahu akbar! Nasan ai ku shaida ne gameda hakan. To gaskiya ba dede bane kuma duk wanda yayi wannan lafazin to ba sallama yayi ba.
Ia sallama anatinta ne ta siga biyu tabbatattu
NA FARKO
Kace 'assalamu alaikum' (bil ma'arfa kenan)
NA BIYU
Kace 'salamun alaikum' (bin-nakirah)
Wadannan sune hanyoyi biyu kacal da ake furta sallama dasu.
Yawanci shi bahaushe baya kula da hakkokin furta wasu abubuwan musamman na larabci, to kuma duk abinda addininmu yakawo mana da harshen larabci yazo. Koda a karatun qur'ani inda zaka fassarawa wani abinda yake cewa wallahi zai iya zubarda hawaye saboda barnar da yakeyi. Yakamata mu dage da neman ilimin larabci kodan furta kalaman alqur'ani da wasu addu'o'in daidai kamar yadda suke a asalinsu.
SASHI NA BIYAR
HUKUNCIN SALLAMA A MUSULUNCI
Kai kayiwa mutum sallama sunnah ne, amma idan kayi masa to shikuma wajibi ne ya amsa.
Amma zakaga bamu kulawa da wannnan sharadin saboda ba kowane yasan hakan ba. yawancinmu bama amsa sallama idan anyi musu, watakila saboda kiwa ko gaba ko girman kai. Hakan kuma saa umarnin shari'ah ne
Alllah yayi umarni da amsa sallama a cikin qur'ani mai girma, inda yace
وَإِذَا حُيِّيتُمْ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا
Ma'ana: idan aka gaishe ka dawata gaisuwa to ku amsa gaisuwar da mafi kyawunta kokuma kumayarda irinta.
Wannan umarni ne. shikuma umarni ana daukarsa ne a matsayin wajibi saide idan ansamu dalilin da zai maida shi mustahabbai.
To maai ake nufi da akace idan an gaisheka kamayar da mafi kyawunta?
Abin nufi shine; idan nazo nace maka 'assalamu alaikum' to kaikuma saikace min 'wa'alaikumussalam warahmatullah'
Idan kuma nace maka 'assalamu alaikum warahmatullah' toh sai kace min 'wa'alaikumussalam warahmaullahi wabarakatuhu'.
Toh mai ake nufi da akace ko kamayar da irinta?
Ana nufin idan nazo nace maka 'assalamu alaikum' to kaima sakace min 'wa'alaikumussalam'.
TAMBAYA
Zakaji wasu idan sukazo zasuyi maka sallama alhalin kuma lokacin kai kadai ne sai kaji sunce maka 'assalamu alaika' (kai kadai kenan)
Malamai sunyi maganganu gameda hakan. Kuma maganar gaskiya bai kamata ba. saboda ai kaidin ba kai kadai bane. Kana tareda mala'iku masu daukar rahoto akanka, toh suma yakamata kahada dasu acikin addu'ar neman amincin.
Wannan shine iyakar abinda nayi nufin rubutawa ga yan uwana musulmi a matsayins ns dan karamin dalibi mai neman ilimi. Ina fata idan malamaina sunga wannan rubutun to zasu fadada bayani game dashi saboda muhimmancin sallama dakuma kasancewarta kalmarda take kewayawa a junanmu kullum.
Ina nan ina jiran gyara ko shawara to tambaya daga gareku gameda wannan rubutun nawa.
Subhanakallahumma wabi hamdik, ash-hadu an la'ilaha illallah wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu.
Wassalam wabillahit-taufiq
Awaisu Haruna Muhammad Al'arabee Fagge FALALAR SAHABBAI
(1) حدثني محمد بن المثنى حدثنا فضل بن مساور ختن أبي عوانة حدثنا أبو عوانة عن الأعمش عن أبي سفيان عن جابر رضي الله عنه
: سمعت النبي صلى الله عليه و سلم يقول ( اهتز العرش لموت سعد بن معاذ )
Ma'ana:- ankarbo hadisi daga jabir dan Abdullahi yace naji manzonn Allah S.W.A. yana cewa: al'arshi tayi girgiza saboda mutuwar sa'ad bin mu'az.
(bukhariy 3592)
Kaga kuwa duk wanda al'arshi zatayi raurawa saboda mutuwarsa ba karamiun bane awajen Allah madaukaki.
(2) حدثنا قتيبة بن سعيد حدثنا محمد بن فضيل عن عمارة عن أبي زرعة عن أبي هريرة رضي الله عنه قال
: أتى جبريل النبي صلى الله عليه و سلم فقال يا رسول الله هذه خديجة قد أتت معها إناء فيه إدام أو طعام أو شراب فإذا هي أتتك فاقرأ عليها السلام من ربها ومني وبشرها ببيت في الجنة من قصب لا صخب فيه ولا نصب
Ma'ana:- abu hurayra yace; manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agare shi yace:- watarana Jibrilu yazo wajena sai yace min ya ma'aikin Allah ga khadija nan zatazo, zata kawo maka kwarya wadda aciki akwai abin sha/abinci, idan tazo kace mata ubangijinta yana gaisheta sannan nima ina gaishe ta sannan kuma kayi mata albishir da gida a aljannah wanda babu hayaniya agidan kuma babu wahala.
(bukhariy 3609)
Dan Allah wacce daraja ce tafi kamar Allah yace yana gaisheka sannan wanda yafi kowa daraja acikin mala'iku?
(3) حدثنا عمرو بن علي حدثنا عبد الأعلى حدثنا خالد عن أبي قلابة قال حدثني أنس بن مالك
: أن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال ( إن لكل أمة أمينا وإن أميننا أيتها الأمة أبو عبيدة بن الجراح )
Ma'ana:- Annabi sallallahu alaihi wasallam yace:-
Hakika kowacce al'umma tana da amintaccenta, amintaccen wannan al'ummar shine ABU-UBAIDAH BIN JARRAH.
(bukhari 3534)
(4) وحدثني الحسن بن علي الحلواني حدثنا جعفر بن عون عن أبي عميس ح وحدثنا عبد بن حميد ( واللفظ له ) أخبرنا جعفر بن عون أخبرنا أبو عميس عن ابن أبي مليكة سمعت عائشة وسئلت
: من كان رسول الله صلى الله عليه و سلم مستخلفا لو استخلفه ؟ قالت أبو بكر فقيل لها ثم من ؟ بعد أبي بكر قالت عمر ثم قيل لها من ؟ بعد عمر قالت أبو عبيدة بن الجراح ثم انتهت إلى هذا
Ma'ana: an tambayi nana Aisha R.A. akace mata wa annabi yake halifantarwa idan bukatar akan ta taso? Sai tace Abubakar, sai akace bayan shi fa? Sai tace Umar. Sai akace mata bayan shi fa? Sai tace Abu ubaidah bin jarrah> sai ta tsaya anan.
(muslim 2385)
(5) حدثنا محمد بن أبي عمر المكي حدثنا مروان بن معاوية الفزاري عن يزيد ( وهو ابن كيسان ) عن أبي حازم الأشجعي عن أبي هريرة قال
: قال رسول الله صلى الله عليه و سلم من أصبح منكم اليوم صائما ؟ قال أبو بكر أنا قال فمن تبع منكم اليوم جنازة ؟ قال أبو بكر أنا قال فمن أطعم منكم اليوم مسكينا ؟ قال أبو بكر أنا قال فمن عاد منكم اليوم مريضا ؟ قال أبو بكر أنا فقال رسول الله صلى الله عليه و سلم ما اجتمعن في امرئ إلا دخل الجنة
Ma'ana:- wata rana annabi yake tambayar sahabbansa yace musu:- yau waye acikinku yawayi gari yana azumi? Sai Abubakar yace gani ya rasulullah. Sai Annabi yace toh waye yawayi gari yarakajana'iza? Sai Abubakar yace gani. Sai Annabi yace toh waye yaciyarda miskini a yau? Sai Abubakar yace gani. Sai annabi yce toh waye yaje duba mara lafiya? Sai Abubakar yace gani ya ma'aikin Allah. Sai annabi yace babu wanda zai hada wadannan abubuwan face sai yashiga aljanna>
(muslim 1028)
(6) حدثني ع?مرو الناقد حدثنا عفان حدثنا حماد ( وهو ابن سلمة ) عن ثابت عن أنس
: أن أهل اليمن قدموا على رسول الله صلى الله عليه و سلم فقالوا ابعث معنا رجلا يعلمنا السنة والإسلام قال فأخذ بيد أبي عبيدة فقال هذا أمين هذه الأمة
Ma'ana:- watarana mutanen yamen sunzo wajen annabi S.A.W. sai sukace masa ya ma'aikin Allah kahada mu da wanda zai koya mana musulunci da sunnah. Sai annabi yakma hannun Abi –ubaidah bin Jarrah yace ga wannan,n shine amintaccen wannan al'ummar
(muslim 2419)
(7) حدثني أحمد بن حنبل حدثنا سفيان بن عيينة حدثني عبيدالله بن أبي يزيد عن نافع بن جبير عن أبي هريرة
: عن النبي صلى الله عليه و سلم أنه قال لحسن اللهم إني أحبه فأحبه وأحبب من يحبه
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam yacewa hassan "ya Allah inason Hassan kaima kaso shi. Sannan kuma kaso duk wanda yaso shi"
(muslim 2421)
Tanbihi:- idan kalura zakaga cewa Abu huraira ne yarawaito wannnan hadisin. Kuma yana daga cikin wadanda yan shi'ah suka dorawa karan tsana.
Anya kuwa makiyin ahlul baiti zai rawaito wannan hadisin?
(8) حدثنا شيبان بن فروخ حدثنا مهدي بن ميمون حدثنا محمد بن عبدالله بن أبي يعقوب عن الحسن بن سعد مولى الحسن بن علي عن عبدالله بن جعفر قال
: أردفني رسول الله صلى الله عليه و سلم ذات يوم خلفه فأسر إلي حديثا لا أحدث به أحدا من الناس
Ma'ana: Abdullahi bin jafar yace wata rana annabi yagoyani abayansa (akan abin hawa) sai yafada min wani sirri wanda ba wanda zan gayaw shi acikin mutane.
(muslim 2429)
(9) حدثنا عبد بن حميد أخبرنا عبدالرزاق أخبرنا معمر عن الزهري عن عروة عن عائشة قالت
: لم يتزوج النبي صلى الله عليه و سلم على خديجة حتى مات
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam bai kara yin sure ba bayan ya auri khadija har saida tamutu.
(muslim 2436)
(10) حدثنا عبد الله بن مسلمة بن قعنب حدثنا سليمان ( يعني ابن بلال ) عن عبدالله بن عبدالرحمن عن أنس بن مالك قال
: سمعت رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول فضل عائشة على النساء كفضل الثريد على سائر الطعام
Ma'ana: anas bin malik yace naji manzon Allah yana cewa "falalar A'isha akan sauran mata kamar falalar 'sarid' ne akan ragowar abinci"
(muslim 2446)
Sarid wani abinci ne wanda yafi kowane abinci daraja awajen larabawa.
(11) وحدثنا أبو بكر بن أبي شيبة حدثنا عبدالرحيم بن سليمان ويعلى بن عبيد عن زكرياء عن الشعبي عن أبي سلمة عن عائشة أنها حدثته
: أن النبي صلى الله عليه و سلم قال لها إن جبريل يقرأ عليك السلام قالت فقلت وعليه السلام ورحمة الله
Ma'ana: watarana Annabi yacewa A'isha "hakika jibrilu yana karanta sallama zuwa gareki" sai nana A'isha tace "shima amincin Allah da rahamars du tabbata gareshi"
(muslim 2447)
(12) حدثني أبو معمر إسماعيل بن إبراهيم الهذلي حدثنا سفيان عن عمرو عن ابن أبي مليكة عن المسور بن مخرمة قال
: قال رسول الله صلى الله عليه و سلم إنما فاطمة بضعة مني يؤذيني ما آذاها
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam yace "fadimah wata tsoka ce daga jikina, abinda yake cutar da ita nima yana cutar dani"
(muslim 2449)
(13) حدثني أبو معمر إسماعيل بن إبراهيم الهذلي حدثنا سفيان عن عمرو عن ابن أبي مليكة عن المسور بن مخرمة قال
: قال رسول الله صلى الله عليه و سلم إنما فاطمة بضعة مني يؤذيني ما آذاها
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam yace "fadimah wata tsoka ce daga jikina, abinda yake cutar da ita nima yana cutar dani"
(muslim 2449)
(14) حدثنا عبد الله قال حدثني أبو صالح الحكم بن موسى نا إسماعيل بن عياش قثنا حميد بن مالك اللخمي عن مكحول عن معاذ بن جبل قال قال لي رسول الله صلى الله عليه و سلم : يا معاذ أطع كل أمير وصل خلف كل إمام ولا تسبن أحدا من أصحابي
Ma'ana:- an karbo hadisi daga Mu'az bin jabal yace" manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace min, yakai mu'az! Kayiwa duk wanda yazamanto shugabanka biyayya, sannan kayi sallah abayan kowanne limami, sannan kuma kada kasake kazagi kowa daga cikin sahabbai na."
(fada'ilus-sahaba 9)
Tanbihi:-
Da annabi yace masa yayiwa shubanasa biyayya hakan yana aiki ne kawai acikin abinda bai sabawa shari'ah ba. saboda shi annabin ya taba cewa ba'a yiwa kowa da'a acikin abinda yazamanto sabon Allah.
(15) حدثنا عبد الله قال حدثني أبي قثنا أبو معاوية قثنا محمد بن خالد الضبي عن عطاء يعني بن أبي رباح قال قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : من حفظني في أصحابي كنت له يوم القيامة حافظا ومن سب أصحابي فعليه لعنة الله
Ma'ana:- ada'u bin abi rabah yace; annabi sallallahu alaihi wasallam yace "duk wanda ya kiyaye min mutuncin sahabbai na toh zan kasance mai kiyaye shi a ranar tashin alkiyama, duk wanda ya zagi sahabbai na kuwa toh tsinuwar Allah ta tabbata agare shi"
(fada'ilyus-sahaba 10)
(16) حدثنا عبد الله حدثني أبي قثنا عبد الرحمن بن مهدي عن سفيان عن نسير بن ذعلوق قال سمعت بن عمر يقول : لا تسبوا أصحاب محمد فلمقام أحدهم ساعة خير من عبادة أحدكم أربعين سنة
Ma'ana:- nusair yace naji umar bin khaddab yana cewa "kada ku zagi sahabban annabi muhammadu, domin kuwa idan dayansu ya tsaya yayi sallah ta awa daya toh tafi ibadar da dayanku xaiyi tsawon shekara arba'in"
(fada'ilus-sahaba 20)
Tanbihi- dama tayaya za'ace bautarka tazamanto daidai data wanda yakoyi bautar daga wajen malaminda Allah ta turo domin koyarda bautar, alhalin kai kuma dorin dosano kazama wajen koyar bauttar taka???
(17) حدثنا عبد الله قال حدثني أبي قثنا أبو معاوية قثنا الأعمش عن أبي صالح عن أبي هريرة قال قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : ما نفعني مال قط ما نفعني مال أبي بكر فبكى أبو بكر وقال وهل أنا ومالي إلا لك يا رسول الله
Ma'ana:- an karbo hadisi daga Abi Hurayra Allah yakara yarda gareshi, yace; manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace "dukkiyar wani bata taba min amfani ba(wajen daukaka kalmar Allah) kamar yadda dukiya Abubakar tamin amfani"
Sai sayyadina Abubakar yace "toh ai ya rasulullah ai dama dani da dukiyav ta ai duk naka ne".
(fada'ilus-sahaba 25)
(18) أَخْبَرَنَا أَبُو عَبْدِ اللَّهِ الْحَافِظُ قَالَ أَخْبَرَنِى أَبُو الْحَسَنِ عَلِىُّ بْنُ أَحْمَدَ بْنِ قُرْقُوبٍ التَّمَّارُ بِهَمَذَانَ حَدَّثَنَا إِبْرَاهِيمُ بْنُ الْحُسَيْنِ حَدَّثَنَا أَبُو الْيَمَانِ أَنْبَأَنَا شُعَيْبٌ عَنِ الزُّهْرِىِّ حَدَّثَنِى سَعِيدُ بْنُ الْمُسَيَّبِ أَنَّ أَبَا هُرَيْرَةَ رَضِىَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- يَقُولُ :« يَدْخُلُ الْجَنَّةَ مِنْ أُمَّتِى زُمْرَةٌ هِىَ سَبْعُونَ أَلْفًا تُضِىءُ وُجُوهُهُمْ إِضَاءَةَ الْقَمَرِ ». فَقَامَ عُكَّاشَةُ بْنُ مِحْصَنٍ الأَسَدِىُّ يَرْفَعُ نَمِرَةً عَلَيْهِ فَقَالَ : ادْعُ لِى يَا رَسُولَ اللَّهِ أَنْ يَجْعَلَنِى مِنْهُمْ. فَقَالَ :« اللَّهُمَّ اجْعَلْهُ مِنْهُمْ ». ثُمَّ قَامَ رَجُلٌ مِنَ الأَنْصَارِ فَقَالَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ادْعُ اللَّهَ أَنْ يَجْعَلَنِى مِنْهُمْ. فَقَالَ النَّبِىُّ -صلى الله عليه وسلم- :« سَبَقَكَ بِهَا عُكَّاشَةُ ».
Ma'ana:- Abu-hurayra yace naji manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana cewa "wata runduna ta mutane dubu saba'in zasu shiga aljannah (daga cikin al'umma ta) fuskarsu tana haske kamar hasken wata", sai Ukkasha yamike yace "ya ma;aikin Allah ka rokar min Allah yasakani acikinsu", sai annabi yace "Allah ka sanyashi daga cikinsu", sai wan mutum ya mike daga cikin mutanen madinah shima yanemi annabi ya rokiu Allah ya sanya shi acikinsu, sai annabi yace "ukkasha ya riga ka"
(sunanul kubrah 20988)
Tanbihi- to ai kai kasan idan annabi ya daga hannu ya roki Allah ai angama. Mu gama garin bayin Allah ma ake amsa addu'armu ballantana shugaban halittun duk duniya da lahira???
(19) حدثنا عبد الله قثنا محمد بن حميد الرازي قثنا إبراهيم بن المختار قثنا إسحاق بن راشد عن الزهري عن عروة عن عائشة أن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال : سدوا هذه الأبواب الشوارع في المسجد إلا باب أبي بكر
Ma'ana:- an karbo hadisi daga Ummuna A'isha Allah yakara yarda gareta tace; manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata a gareshi yace "ku tottoshe wadannan kofofinda kukayi (wadanda suke kawo ku masallaci kai tsaye daga gidajenku) sai de kofar Abubakar (ita abarta basai an rufe ba)"
(fada'ilus-sahaba 33)
Tanbihi- wannan yana daya aga cikin isharorinda annabi yake na cewa Abubakar shine zai kasance khalifa bayan annabi.
(20) حدثنا عبد الله قال حدثني هارون بن سفيان البرتي قثنا بشر بن عبيس بن مرحوم قثنا النضر بن عربي عن عاصم عن سهيل عن محمد بن إبراهيم عن أبي سلمة بن عبد الرحمن عن أبي أروى الدوسي قال : كنت مع النبي صلى الله عليه و سلم جالسا فطلع أبو بكر وعمر فقال رسول الله صلى الله عليه و سلم الحمد لله الذي أيدني بكما
Maa'ana:- abi urwa yace wata rana muna zaune tareda annabi sai Abubakar da Umar suka taho, sai annabi yace "ina godiya ga Allah wanda ya karfafeni da wadannan mutum biyun"
(fada'ilus-sahaba 37)
Tanbihi- wannan shine abinda Allah yafada awata aya a alkur'ani mai girma, Allah yace:-
وَإِنْ يُرِيدُوا أَنْ يَخْدَعُوكَ فَإِنَّ حَسْبَكَ اللَّهُ هُوَ الَّذِي أَيَّدَكَ بِنَصْرِهِ وَبِالْمُؤْمِنِينَ
Ma'ana:- idan (munafukai) sunyi nufin su yaudareka ko su ha'ince ka toh Allah zai isar maka daga sharrinsu, (wannan Allahn dai) wanda ya karfafeka da taimakonsa(a yakin badar) dakuma muminai.
Wallahu a'alam. Wal ilmu indallah.
(21) حدثنا عبد الله قثنا صالح بن عبد الله الترمذي قثنا حماد بن زيد عن عاصم بن أبي النجود عن زر بن حبيش عن أبي جحيفة قال سمعت عليا يقول : ألا أخبركم بخير هذه الأمة بعد نبيها أبو بكر ثم قال ألا أخبركم بخير هذه الأمة بعد أبي بكر عمر
Ma'ana:- abi juhaifa yace naji Aliyu yardar Allah ta kara takara tabbata gareshi yana cewa "ku saurara nagaya muku wanda yafi kowa alkhairi acikin wannan al'ummar bayan manzon Allah, wannan kuwa shiine Abubakar, kun saurara nafada muku wanda yafi kowa alkhairi bayan Abubakar acikin wannan al'ummar, wannan kuwa shine Umar "
(fada'ilus-sahaba 40)
(22) حدثنا عبد الله قال حدثني أبو الفضل الخراساني قثنا معلى بن أسد قثنا هلال بن عبد الرحمن الأزدي قال حدثني علي بن زيد وعطاء بن أبي ميمونة عن أنس بن مالك قال : كان النبي صلى الله عليه و سلم يدخل بيت أبي بكر كأنه يدخل بيته ويصنع بمال أبي بكر كما يصنع بماله
Ma'ana:- annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam yakasance yana shiga gidan sayyadina Abubakar kai tsaye kamar yanda yake shiga gidansa, sannan kuma yanayin tasarrufi da dukiyar Abubakar kamar uanda yake yake tasarrufi da dukiyarsa.
(fada'ilus-sahaba 65)
(23) حَدَّثَنَا مُحَمَّدٌ حَدَّثَنَا عَفَّانُ عَنْ صَخْرِ بْنِ جُوَيْرِيَةَ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ الْقَاسِمِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ دَخَلَ عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ أَبِي بَكْرٍ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا مُسْنِدَتُهُ إِلَى صَدْرِي وَمَعَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ سِوَاكٌ رَطْبٌ يَسْتَنُّ بِهِ فَأَبَدَّهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَصَرَهُ فَأَخَذْتُ السِّوَاكَ فَقَصَمْتُهُ وَنَفَضْتُهُ وَطَيَّبْتُهُ ثُمَّ دَفَعْتُهُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَاسْتَنَّ بِهِ فَمَا رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ اسْتَنَّ اسْتِنَانًا قَطُّ أَحْسَنَ مِنْهُ فَمَا عَدَا أَنْ فَرَغَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَفَعَ يَدَهُ أَوْ إِصْبَعَهُ ثُمَّ قَالَ فِي الرَّفِيقِ الْأَعْلَى ثَلَاثًا ثُمَّ قَضَى وَكَانَتْ تَقُولُ مَاتَ بَيْنَ حَاقِنَتِي وَذَاقِنَتِي
Ma'ana:- nana Aisha R.A. tace "(dan uwana) Abdullahi bn Abibakar ya shigo wajen Annabi SAW alhalin lokacin yana jingine a kirjina, a hannun Abdullahi akwai wani danyan aswaki yana goge bakinsa da shi, sai naga annabi SAW ya kura masa ido, sai na amshi aswakin na juya can kasan da ba'a taunaba sai na tauna sannan na tsarkake shi sannan na mikawa annabi shi, ban taba ganin annabi yana goge hakoransa ba kamar yadda naga yayi a wanan ranar, bai dena aswakin nan ba har sai lokacinda ya daga hannunsa/dan yatsansa sama yana cewa ina tareda 'rafiqil a'ala' " tace annabi ya mutu yana tsakanin kirji da hakarkari na.
(bukhariy 4438)
(24) حَدَّثَنَا الْمُنْذِرُ بْنُ الْوَلِيدِ الْجَارُودِيُّ ، قَالَ : حَدَّثَنَا أَبِي ، قَالَ : حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ أَبِي جَعْفَرٍ ، عَنْ عَاصِمٍ ، عَنْ زِرٍّ يَعْنِي ابْنَ حُبَيْشٍ ، عَنْ عَمَّارِ بْنِ يَاسِرٍ ، قَالَ : لَمَّا طَلَّقَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم حَفْصَةَ ، أَتَاهُ جِبْرِيلُ صلى الله عليه وسلم ، فَقَالَ : رَاجِعْ حَفْصَةَ فَإِنَّهَا صَوَّامَةٌ قَوَّامَةٌ ، وَإِنَّهَا زَوْجَتُكَ فِي الْجَنَّةِ.
Ma'ana:- an karbo hadisi daga Ammar bin yasir, yace "lokacinda Annabi SAW ya saki Nana Hafsatu, sai mala\ika jibrilu yazo masa yace masa "kamaida ita domin ta kasance mai yawan azumin nafila kuma mai yawan tsayuwar dare ce kuma sannan matar ka ce a gidan aljannah".
(musnad bazzar 1404) ALAQAR SAHABBAI DA AHLULBAYTI
Awani lokacin kuma kalmar (ال) ko (أهل) tana zuwa da ma'anar wdanda suke dauke da wani abu, abin nufi anan shine duk abinda kake dauke dashi toh kai ahalin abin ne. misalin wannnan kuwa zamu same shi ne acikiin wata aya a alqur'ani mai girma inda Allah yace
فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Ma'ana: Allah yace kutambayi ma'abota sani in har baku sani ba.
Kaga anan sun zamto ma'abota/madauka ilimine shi yasa aka jingina musu kalmar (أهل).
Awani wajen kuma Allah madaukaki yace:-
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ
Ma'ana:(yakai ma'aikin Allah) kace musu yaku ma'abota littafi kuzo mana muhadu akan wata kalma wadda zatayi daidai tsakaninmu daku.
Kaga anan ma mun kara samun tabbacin cewa kalmar tana iya zuwa da ma'anar abinda wani yake dauke dashi.
A wani lokacin kuma kalmar (أهل) tana zuwa da ma'anar mazauna wani wuri, tana yawan zuwa da wannan ma'anar acikin alqur'ani dakuma gama garin larabci nayau da kullum.
Misalin haka yazo acikin wata aya kamar haka:-
وَجَاءَ أَهْلُ الْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ
Ma'ana: sai mutanen/mazauna garin sukazo(gidan Annabi Lud) sunata yiwa junansu bushara(da aikinda suka saba sunayi).
Ana zamu fahimci cewa kalmar tazo da ma'anar mazauna garin.
Awani lokacin kuma kalmar (أهل) tana zuwa da ma'anar matar mutum. Kamar yadda yazo acikin littafin (مفردات كلمات القران الكريم) na al-asbihaniy. Yace larabawa sune cewa (أهل فلان) toh ana nufin (زوخة أو إمرأة) wato ana nufin matarsa.
Larabawa ma sune cewa (فلان تأهل) da ma'anar (تزوج). Wato suna cewa wane yayi iyali alokacinda mutum yayi aure.
Toh kaga wadannan ma'anonin da muka ambata daga farko zuwa yanzu sun nuna mana ire-iren abubuwanda kalmar tace iya dauta.
Idan akace (أهل البيت) mai ake nufi a larabci?
Da farko dai fassarar kalmar da hausa shine iyalan gida.
Kamar yadda malam al-asbihaniy yafada a littafinda muka ambata abaya yace; idan akace (أهل بيت فلان) iyalan gidan wane, ana nufin (من يجمعه و إياهم مسكن واحد) shine wadanda suke zaune acikin gidanka a karkashinka, wadannan sune ahalinka. Kenan duk wanda yake zaune karkashin jagorancinka kuma acikin gidanda to alarabce yazama ahalin gidanka.
Toh kamar yadda al'adar yarirrika take; ana samun aron ma'anar kalmomi daga wani abun zuwa wani bun na daban, hakanne yasa akayi aron wannan ma'anar dana ambata abaya aka yi mata (المجازى التعريف) aka aroma'anar aka mayarda ita akan (من جمعه وإياهم نسب) wato duk wanda dangantaka ta jini kokuma duk wanda kuka fito ta tsatso daya. Hakan ma'anar takoma daga baya, amma da a asalin larabci basu bane ahalinka.
Wannan kuwa koda ayarenmu na hausa idan akace iyalin mutum akarin fari ana nufi matarsa sannan yayansa subiyo baya. Shiyasa idan aka wayi gari akaga mutun magidanci dasafe a teburin mai shayi yana karin kumallo sai atambayeshi ace 'wane iyalin basa nan ne?'
Koda alkur'an mai girnma ya goyi bayan wannan wannan ma'anar baya kamar yadda yatabbat kamar haka:-
Kalmar (أهل) tana zuwa da ma'anar matan mutum, ga misali daga cikin alkur'ani mai girma. Allah yace
وَإِذْ غَدَوْتَ مِنْ أَهْلِكَ تُبَوِّئُ الْمُؤْمِنِينَ مَقَاعِدَ لِلْقِتَالِ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Ma'ana:- ka tuna (ya kai manzon Allah) lokacinda kayi sammakon fitowa daga wajen iyalanka domin ka tsarawa muminai wajenda zasu tsaya domin tunkarar arna (a yakin uhudu kenan), Allah maiji ne kuma mai masanine da abinda yafaru a lokacin.
Wannan ayar tanuna mana cewa ana kiran matan mutum ahalinsa.
Daga cikin dalilan da suke nuna cewa (أهل) tana daukar ma'anar matan mutum akarin fari, akwai aya da Allah yasaukar acikin suratu nur, Allah yace:-
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّى تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَى أَهْلِهَا
Ma'ana:- yaku wadanda suka bada gaskiya kada ku shiga gidajenda ba naku ba har sai kunyisallama sannnan kun nemi iso ga ahalin gidan.
Toh abin tambaya ana shine; suwanene suke xaune agidajen?? Ai matan mutun ne dakuma yayansa in akwai.
Kaga kenan wannan ayar ma takara tabbatar mana da ma'anar.
Awata ayar kuma Allah yace
إِذْ رَأَى نَارًا فَقَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا
Ma'ana:- (Allah yana bada labarin annabi musa) yayinda ya hangi wuta, sai yacewa matarsa "tsaya anan"………..
Wannan ayar ma takara tabbatar mana da abinda muka fada abaya.
(kada ka manta fa har yanxuu muna bayanin kalmar ne a mahangar yare)
A shari'ance kuwa idan akace (أهل بيت رسول الله) ana nufinwadannan dai wadanda suke zaune acikin gidansa, matansa da yayansa kenan, toh yayan maza kuwa dama duk sun riga sun koma ga Allah tun suna yan kanana, matan kuwa wasu sun koma ga Allah wasu kuwa suna gidajen mazajensu na aure.
Kaga kenan iyalan annabi sune matansa da yayansa dakuma tsatsonsa wadanda ya lissafa a hadisi yace haramun ne suci sadaka, sai kuma wadanda idan akabi nasabarsu tana tikewa izuwa gidan JA'AFAR BIN ABDULMUDDALIB, ABBAS BIN ABDULMUDDALIB, ALIYU BIN ABI DALIB da kuma AKILU BIN ABI DALIB. Wadannan gidajen guda biya in ka hada harda annabi sune ake cewa 'iyalan gidan annabi SAW'.
Toh kafin mucigaba, danganeda wannadan 'definations' din da muka bayar, wanda duk malaman musulunci dashi suka yarda kuma suka aminta, sai aka sami wasu jama'ah masu jingina kansu zuwaga addinin musulunci sukace bahaka ma'anar take ba. sukace dafarko dai matan annabi SAW ba ahlulbaiti bane, saboda me?? Saboda suna da aqidar zagin nana Aisha da Hafsa, da ragowar matana annabi SAW, musamman guda biyun da na ambata abaya. Wanda su awajensu ma addini ne ian ka tashi daga barci kullum saika tsinewa mutum hudu sannan imaninka yazama cikakkce, wanda ake tsinewa din kafin addinin shi'ah ya cika sune Abubakar da Umar da yayansu mata guda biyu wato A'isha da Hafsa.
Tho su wadannan mutanen sunata yayata wa cewa matan annabi ba ahlulbayti bane, toh idan muka koma kur'ani kuwa zamu samu bayanin cewa tana zuwa da ma'anar, kamar dai irin bayaninda mukayi abaya. Amma dai tunda hausawa sunce kogi bayakin dadi, toh bari mu dan kara bayani ko abin zai kara fitowa fili yan uwa su fahimta.
A lokacinda matar sarkin misra ta nemi annabi Yusuf da yayi alfasha da ita shikuma yaki, ai tabiyoshi shikuma ya gudu, kwatsam sai gasu agaban mijinta (sarkin misra) nan take sai tace:-
قَالَتْ مَا جَزَاءُ مَنْ أَرَادَ بِأَهْلِكَ سُوءًا
Ma'ana:- (lokacinda taga mijintaa gabanta ) sai tace "menene hukuncin wanda yanemi ya aikata wani mummunan aiki da iyalinka???"
Suwaye iyali a wannan ayar??? Ai mata ce.
Awata ayar kuma Allah yace:-
قَالُوا أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ اللَّهِ رَحْمَتُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ
Ma'ana:- (a lokacinda mala'iku sukazo suka kawowa annabi Ibrahim ziyara, sai kuayi masa albishir da cewa zai sami da, toh shikuma lokacin dashi da matarsa duk sun tsufa sun wuce lokacin haihuwa na al'ada, da akayi musu busharar samun dan dai matar take mamaki, sai mala'ikun sukace mata) shin kimna mamakine daga al'amarinn ubangiji??? Ai wannan abin rahamace gareku yaku ahlulbait.
Ai su biyu ne dai ko da basu dashi, kenan waye ahlulbaity??? Wadda tayi mamaki da abinda aka fada itace ahlulbayti.
A lokacinda abu yayi tsamari tsakaninannabi Musa da fir'auna, yanayi yasa dole sai annabi Musa yabar garin Misra. Nan take ya kama hanyarsa ta zuwa garin Madyana. Zuwansa ke da wuya sai yaga wasu yammata suna gefe a zaune, can kuma ga jama'a suna diban ruwa a rijiya, sai yaje ya tambayi wadannan yammatan yace musu "mai yasa naga mutane suna diban ruwa amma ku kuma kuna gefe a zaune???"
Sai yammatan sukace masa "mu aii bama zuwa diban ruwa harsai mazan sun gama sannan mu zamu je"
Nan take annabi Musa yaje ya debo musu ruwan ya basu sannan kuma kama hanya suka tafi gida. Da sukaje gidan sai suka bada labarin abinda yafaru, sai akace dayarsu taje ta kirawo shi. Bayan ta kirawo shi ajarshe sai mahaifinsu ya bayyanawa annabi Musa cewa yanaso ya aura masa daya daga cikin yayan nasa a bisa sharadin zaiyi masa kiwo na shekara takwas, bayan Annabi Musa ya kammala kiwon, sai ya dauki matarsa da niyyar suzo Misra ganin gida, da Allah ya tashi labarta mana abinda ya faru, sai Allah yace:-
فَلَمَّا قَضَى مُوسَى الْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِ آنَسَ مِنْ جَانِبِ الطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آنَسْتُ نَارًا
Ma'ana:- yayinda annabi Musa ya cika wa'adin da aka diba masa, sai yayi tafiya da ahalinsa, (suna cikin tafiyar bayan hanya ta bace musu) ai ya hango wuta tanaci a gefen dutse, sai ya cewa ahalinsa tsaya ana bari inje in samo mana wutar (domin muji dumi).
Toh abin tambaya anan shine:- wacece ahalinsa??
Amsa: matarsa tunda ita kadai garshi a wanna lokacin.
Awata ayar kuma Allah yace
…………….إِذْ رَأَى نَارًا فَقَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا
Ma'ana:- (Allah yana bada labarin annabi Musa) yayinda ya hangi wuta, sai yacewa matarsa "tsaya anan"………..…..
Wannan ayar ma takara tabbatar mana da abinda muka fada abaya.
Bisa la'akari da hujjoji da muka kawo abaya, wani zai iya cewa ai wannan duk ana magana ne akan al'ummominda suka gabace mu.
Domin Allah ya magance wannan matsalar, da Allah yazo magana da matan annabi sai yace musu:-
وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا
Ma'ana:- ku zauna ku tabbata acikin gidajenku, kada ku dinga yawan fita irin fitar matan jahiliyya. Sannan ku tsaida sallah kuma ku bayarda zakkah, kuma kuyiwa Allah da manzon Allah da'a, (wadannan dokokinda Allah yasaka muku, bawai anyi ne domin a takuraku ba, a'a, abinda yasa akayi hakan shine) hakika Allah yanaso ya kore datti (na zunubi da sabo) daga gareku ne yaku AHLULBAYTI, kumaAllah yanaso ne ya tsarkake ku matukar tsarkakwa.
Wannan ayar ta tabbatar mana da cewa matan annabi suma ahlulbayti ne.
Toh anan ne sai sudai (yan shi'ah) suke cewa toh ai ba haka ayar take nufi ba saboda ai farkon ayar duk kalmomin suna zuwa ne da lakabinda ake amfani dashi akan mata kamar haka, (وَقَرْنَ), (بُيُوتِكُنَّ), (تَبَرَّجْنَ), (وَأَقِمْنَ), (وَآتِينَ), (وَأَطِعْنَ) ai duk sun kare da (ن) kuma lakabin mata ne, amma ai da akazo maganar ahlulbaitun sai da lakabin maza akayi amfani, domin cewa akayi (عَنْكُمُ) wannan kuma alamace da take nuna cewa da maza ake magana.
Allah akbar, toh ai abinda yasa kukayi musun wadannan bayanai abu biyu n.
NAFARKO- kun jahilci alkur'ani mai girma, domin kuwa ai duk wanda yasan kur'ani yasan farkon ayoyinda aka jero yanada alaka a karshensu, kuma hakan bazai taba canjawa ba idan kuwa har kace zai canja toh kenan kana tuhumar kur'ani da gwaranci.
Zan kawo jerin ayoyin a jeransu ba tareda na fassara ba, domin kawai inaso a fahimci herin nasu kamar yadda yazo a kur'ani mai girma.
Ga abinda Allah yace:-
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأَزْوَاجِكَ إِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيْنَ أُمَتِّعْكُنَّ وَأُسَرِّحْكُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا (28) وَإِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالدَّارَ الْآخِرَةَ فَإِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِنَاتِ مِنْكُنَّ أَجْرًا عَظِيمًا (29) يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ مَنْ يَأْتِ مِنْكُنَّ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ يُضَاعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَيْنِ وَكَانَ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا (30) وَمَنْ يَقْنُتْ مِنْكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِ وَتَعْمَلْ صَالِحًا نُؤْتِهَا أَجْرَهَا مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنَا لَهَا رِزْقًا كَرِيمًا (31) يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا (32) وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا (33) وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا
Idan har kana zuwa makaranta kuma ka karanta wadannan ayoyin a yadda suke toh zaka fahimci daga farkonsu har karshe suna magana ne da matan annabi.
ABU NA BIYU- rashin sanin ka'idojin labarci ma yana daya daga cikin dalilin dayasa kuka kasa fahimtar nassi.
Domin kuwa a ka'idar larabci idan ana magana da maza damata toh ana yin amfani ne da lakabin maza koda kuwa matan sunfi yawa.
Ayoyin sun sauka ne akan matan annabi SAW toh amma dayake ba su kadai bane ahlulbaiti akwai maza, sai akayi amfani da lakabin maza.
Idan kuwa kace kai baka yarda ba, sai muce maka indai wannanb ayar tana nuna cewa mata ba ahlulbaitu bane, toh kenan kayiwa kanka da kanka raddi, domin kuwa nana Fadima ba ahlulbayti bace tunda itama mace ce.
Allahu akkbar!!!! Hujjah takobin ahlussunnah.
Saboda da haka su ragowar maza ahlulbaiti wadanda muka lissafa abaya sun shiga rigar martaba tamatan annabi ne shiyasa suma suka sami wannan falalar ta tsarkakewa daga Allah madaukaki.
Domin Annbi ya nuna maka cewa ragowar mazan sun shiga rigarmatan ne sai annabi yanuna mana a wani hadisi da muslim ya rawaito daga NANA AISHA, ga hadisin
حدثنا أبو بكر بن أبي شيبة ومحمد بن عبدالله بن نمير ( واللفظ لأبي بكر ) قالا حدثنا محمد بن بشر عن زكرياء عن مصعب بن شيبة عن صفية بنت شيبة قالت قالت عائشة
: خرج النبي صلى الله عليه و سلم غداة وعليه مرط مرحل من شعر أسود فجاء الحسن بن علي فأدخله ثم جاء الحسين فدخل معه ثم جاءت فاطمة فأدخلها ثم جاء علي فأدخله ثم قال إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا
Ma'ana:- (bayan Allah madaukaki ya saukar da wannan ayar watarana sai)annabi ya annabi ya fito (tsakar gidansa) da wani bakin mayafi, sai HASSAN yazo, sai annabi yasanya shi aciki, sai HUSSAINI yazo shima aka sakashi aciki, sai NANA FADIMA tazo itama yasakata aciki, sai ALIYU yaazo shima kaka sakashi aciki, (sai annbi yayi musu addu'ah sannan)
Ya karanto wannan ayar wadda tasauka akan matansa da niyyar Allah yahada da wadannan wanda ya lullube su a mayafi acikin falalar ayar.